An shigar da karar kafafan yada labarai Kotu saboda harin Faransa
Wasu mutane 6 sun shigar da karar kafafan yada labarai na Kasar Faransa Kotu, sakamakon zarginsu da laifin haska hotan bidiyon su a lokacin da ‘yan bindiga suka kaddamar da hari a kamfanin mujallar Charlie Hebdo
Wallafawa ranar:
Kafafan yada labaran sun dau hotan bidiyon mutanen bayan sun buya a dakin na’urar sanyaya abinci ta Kantin Kosher dan gudun salwantar rayukansu a harin da ‘yan bindigan suka kai a kamfanin barkonci na Mujallar Cahrlie Hebdo a watan Janairun wannan shekarar.
Mutanen sun zargi kafafan yada labaran da nuna wa duniya inda suka buya kai tsaye, yayin da suka ce, hakan nada hatsarin gaske, lura da cewa, a dai dai lokacin ne, daya daga cikin ‘yan bindigan mai suna Amedy Coulibaly ya kutso kai cikin kantin, inda nan take ya bude wuta tare da kashe mutane 4 a Kantin.
Idan har an sami kafofin yada labaran da laifi, ana iya zantar masu da hukuncin dauri na tsawon shekara guda ko taran kudi Euro dubu 15.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu