Isa ga babban shafi
Ukraine

Wasu hare hare sun yi sanadiyyar mutuwar sojoji 6 a kasar Ukraine

Sojojin gwamnatin Ukraine 6 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare biyu mabambanta da aka kai masu yankin gabashin kasar mai fama da rikici. Da farko sojoji 4 ne suka rasa rayukansu bayan da aka harbo wata roka a motar da suke tafiya a cikinta kusa da Lugansk, yayin da wasu sojojin 2 suka mutu bayan da motarsu ta taka nakiya a wani wuri da ba ya da nisa da birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa, kamar dai yadda mai magana da yawun rundunar sojan kasar Oleksandr Motuzyanyk ya tabbatar.Duk wannan na zuwa ne makonni bayan da aka fara tunanin yarjejeniyar tsagaita wutar dake tangal tangal, ta fara aiki sosai, duk da ‘yan tashe tashen hankulan da ake samu a wasu wuraren.Kisan wadannan sojojin ya sa yawan dakarun kasar da aka hallaka suka kai 9, cikin makonni 2.Dama shugaba Petro Poroshenko ya nemi a kai dakarun wanza da zaman lafiya, don daidaita lamura a cikin kasar ta Ukraine.Zuwa yanzu rikicin n Ukraine ya lakume akallar rayukan munate dubu 6 a fadin kasar. 

Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko REUTERS/Valentyn Ogirenko
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.