MDD ta damu game da jinkirin isar da kayan agaji a Nepal
Hukumar kula da lafiya al-umma ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan jan kafar da hukumar Kwastam ta Kasar ke yi dangane da isar da kayayyakin agaji ga wadanda bala’in girgizar Kasa ta shafa a Kasar Nepal
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da lafiyar ta bukaci Firaministan Kasar ta Nepal, Sushil Koirala daya dau matakin shawo kan matsalar jinkirin isar da kayayyakin agajin.
Rahotannni sun bayyanna cewa, an jibge kayayyakin agaji da aka aiko daga kasashen ketere a wani karamin filin tashi da saukan jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Kathmandu, yayin da kuma jami’an kwastam ke mayar da kayayyakin a kan iyakar kasar da India.
A ranar asabar din data gaba ta ne girgizar kasar ta auku kuma kawo an rasa rayukan mutane sama da dubu 6 baya wadanda suka rasa gidajeensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu