Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta fara sauraren shari'ar matar da ta kashe 'ya'yanta

Wata Kotu a kasar Faransa ta fara sauraren shari’ar da ake yiwa wata mata da ta kashe 'ya'yanta guda 8 da zaran ta haife su.

Ma'aikatan shari'a a Faransa
Ma'aikatan shari'a a Faransa AFP PHOTO MARTIN BUREAU
Talla

Matar mai suna Dominique Cottrez, mai shekaru 51 wadda tsohuwar ma’aikaciyar lafiya ce, ta amsa tambayoyi a kotun amma taki cewa komai game da mahaifinta wadda a baya tace shine uban 'ya'yan na ta.

Kotun ta saurari bayanin cewar matar kan shake jirajiran na ta ne har sai sun mutu da zaran ta haife su tsakanin shekarar 1989 zuwa shekara ta 2000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.