Isa ga babban shafi
MH370

Faransa ta zurfafa binciken jirgin Malaysia MH370

Kasar Faransa tace ta sake kaddamar da aikin neman inda jirgin saman Malaysia kirar MH370 ya fadi kusa da Reunion daga yau juma’a, bayan Malaysia ta tababtar da cewar sashen jirgin da aka samu a gabar teku daga jikin jirgin da ya bata ne.

Mafi yawancin Fasinjan da ke cikin Jirgin Malaysia MH370 da ya bata 'Yan China ne
Mafi yawancin Fasinjan da ke cikin Jirgin Malaysia MH370 da ya bata 'Yan China ne REUTERS/Jason Lee
Talla

Gwamnatin Faransa tace jirgin saman sojin kasar zai fara aikin neman jirgin yau da safe, wanda daga bisani zai samu taimakon sojojin kasa, da jiragen sama masu saukar ungulu da kuma jiragen ruwa.

Ministocin tsaro, da sufuri da mai kula da kasashen waje mallakar Faransa za su sanar da duk wani abin da binciken ya gano ga jami’an binciken hadarin.

Wannan kuma na zuwa a yayin da dangin wadanda ke cikin jirgin suka kaddamar da zanga-zanga a ofishin jekadancin Malaysia a China.

‘Yan uwan Fasinjan sun bukaci a tafi da su tsibirin Reunion inda aka tsinci wani bangare da ake hasashen na Jirgin ne da ya bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.