Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya karrama Fasinjojin da suka murkushe dan bindiga

Shugaban Kasar Faransa Fraoncois Hollande ya karrama wasu Fasinjojin uku da suka murkushe wani dan bindiga da ya kai hari a cikin wani jigin Kasa a Faransa.Wannan kyauta dai ta kasance mafi girma a jerin kyautar da Kasar ke bayarwa.

Shugaban Faransa François Hollande.
Shugaban Faransa François Hollande. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Fasinjojin da aka karrama sun hada da Amurkawa Biyu da dan kasar Ingila.

Faransa ta bayyana Fasinjojin a matsayin Jarumai lura da kokakrin da suka yi na murkushe dan Bindigan mai suna Ayoub El-khazani, duk da irin bindigan da ya ke dauke da shi da kuma mugan makaman da ke cikin jakarsa.

Akwai wani dan Faransa da shima ya taimaka wajan cin Karfin El-Khazani, to sai dai ya nemi a Sakaya sunansa, amma gwamantin ta mashi alkawarin ta sa kyautar wani lokaci nan gaba.

Maharin dai ya musanta cewa harin nasa na da alaka da ta’addanci.

To sai dai shaidun gani da ido sun tabbartar da cewa El-khazazani ya bude wuta da bindigar da ke hannusa tare da raunata mutane biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.