Isa ga babban shafi
Romania

Romania na juyayin mutuwar mutane 27

Kasar Romania na juyayin mutuwar mutane 27 da suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan rawa da ke babban birnin Bucharest a yau asabar wadda kuma ta jikkata kimanin mutane 200.

Jami'an tsaro na daukar da gawarwaki bayan aukuwar gobarar
Jami'an tsaro na daukar da gawarwaki bayan aukuwar gobarar REUTERS/Inquam Photos
Talla

Gwamantin kasar dai ta ware kwanaki uku domin zaman makoki a duk fadin kasar.

Firaiministan kasar Victor Ponta ya ce, baki daga kasashen ketere na cikin wadanda lamarin ya ritsa da su, da suka hada da ‘Yan kasashen Spain da Italiya da kuma Jamus.

To sai dai shaidu sun bayyana cewa, wasu matasa ne suka rika yin wasan wuta a cikin gidan rawa, kuma daga nan ne gobarar ta tashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.