Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan sanda sun bindige wani mutum a Faransa

‘Yan sanda a birnin Paris na Faransa sun bindige wani mutum da ya tunkare su dauke da wuka a hannunsa, a dai-dai lokacin da ake bukukuwan cika shekara daya da kai wa ginin mujallar Charlie Hebdo hari a bara warhaka.

'Yan sanda a Faransa
'Yan sanda a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Bayanan farko da ‘yan sanda suka fitar na nuni da cewa maharin ya yi kokarin kutsawa a cikin ginin ofishin ‘yan sandar, kuma a lokacin yana dauke da wata jigida ta bama-bamai, wadda bayan an harbe shi aka gano cewa ta jigidar ta jabu ce.

Hakazalika maharin na dauke da wuka da wata ‘yar karamar jaka, to sai dai ‘yan sandan sun musunta cewa yana dauke da bindiga a lokacin da ya tunkare su.

Lamarin dai ya faru ne yayin da Faransawa ke tunawa da zagayowar ranar da aka kai wa ginin Mujallar Paris Hebdo hari a ranar 7 ga watan janairun shekarar bara, yayin da a hannu daya shugaban kasar Francois Hollande ke gabatar da jawabi a gaban wasu manyan jami’an soja, jandarma da kuma ‘yan sanda a yau.

Inda ya bukaci goyon bayan al’ummar kasar domin fada da ayyukan ta’addanci.

Shekarar da ta gabata dai ta kasance mummuna ga Faransa, sakamakon hare-haren da aka kai wa kasar da suka hada da na Charlie Hebdo da kuma wani a watan nowambar da ya gabata inda mutane 130 suka hallaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.