Isa ga babban shafi
Rasha

Takukumin kasashen Yammaci na yi mana illa-Putin

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana cewa takukumin kariyar tattalin Arzikin da kasashen yammaci suka kakabawa kasar sakamakon rikicin Ukraine ya gurgunta tattalin Arzikin kasar matuka

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Poutine
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Poutine REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

A hirara sa da jaridar German daily putin ya ce duk da damar da suke da su a kasuwannin kasashen Duniya, wannan matakin na kawo musu koma baya ainun.

A cewar Putin, Rasha na tabka asarar kudaden shiga a kasuwar hada-hadar mai da iskar Gas, abin da ya zama musu wajibi su cike gibin daga wasu kafofin.

Rasha dai na fuskantar takunkumin ne daga turai da Amurka sakamakon rawar da take takawa a rikicin Ukraine wanda ke sanadi rayuka mutane da dama.

A watan Disamban bara dai kungiyar tarayyar Turai ta sake tsawaita takukumin zuwa watanni 6, abinda ya sake jefa tatalin Arzikin Rasha cikin mawuyacin hali.

Amma inji Putin suna ‘yan dabarun farfado da tattalin Arzikin kasar

A karon farko dai cikin shekaru Rasha na fidda kayayyaki kasashen waje amma da dinbin haraji.

Kuma Rashan na da kudin da suka haura dala biliyan Uku na cinikin zinare a asusun ajiyar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.