Isa ga babban shafi
Faransa

Kananan hukumomin Faransa 800 na halin tsaka mai wuya

Gwamnatin Faransa ta bayyana kananan hukumomi 800 da ke kasar a matsayin wadanda al’ummominsu ke rayuwa a cikin hali na tsaka-mai-wuya, sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da kuma ambaliya da suka shafi yankunan.

Ambaliyar ruwa ta Jefa kananan Hukumomin Faransa 800 halin tsaka mai wuya
Ambaliyar ruwa ta Jefa kananan Hukumomin Faransa 800 halin tsaka mai wuya
Talla

Sanarwar da aka fitar bayan kammala taron majalisar ministocin kasar a wannan laraba, ta bayyana kananan hukumomi 782 daga jihohi 16 a matsayin wadanda bala’I ya shafa.

Ministan cikin gidan kasar Bernard Cazeneuve, ya ce akwai yiyuwar adadin yankunan da bala’in ya shafa zai karu, domin yanzu haka suna nazari kan halin da ake ciki a wasu yankunan kasar 215.

A birnin Paris, wannan ne karo na farko tun shekarar 1982, da aka samu ambaliyar ruwa irin wadda aka gani a bana, lamarin da ya sa aka rufe wasu makarantu, gidajen yari, da kuma babban gidan ajiye kayayyakin tarihi na Louvre da kuma Orsay.

Alkauluman da kamfanonin inshore na Faransa suka fitar, na nuni da cewa ambaliyar ta haddasa asarar dukiya ta sama da Euro bilyan daya da milyan 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.