Isa ga babban shafi
Faransa

Kamfanin Lafarge na Faransa yana kawance da IS

Wani Kamfanin Siminti na Faransa Lafarge ya kulla yarjejeniya da mayakan IS masu da’awar jihadi a Syria, domin kare manufofin kasuwancinsa a cikin kasar mai fama da yaki.

Kamfanin Siminti na Lafarge na kawance da IS masu da'awar Jihadi a cewar Jaridar Le Monde
Kamfanin Siminti na Lafarge na kawance da IS masu da'awar Jihadi a cewar Jaridar Le Monde AFP/ FRANCK FIFE
Talla

Jaridar Le Monde ce ta ruwaito labarin, kuma ta ce kamfanin na Lafarge ya kulla yarjejeniya da kungiyoyin da ke yaki a Syria ciki har da kungiyar IS da ke iko da wasu yankuna a kasar.

Jaridar tace kamfanin Simintin na Faransa ya shiga kawance ne da IS don ci gaban kasuwar shi da kuma kariyar tsaro da ma’aikatansa.

Le Monde tace yarjejeniyar da Lafarge ya kulla ta shafi wani kamfanin simintin Jalabiya ne da ya saya a 2007 a arewa maso gabashin Aleppo.

Kuma jaridar ta ruwaito cewa ta ga takardar yarjejeniyar da kamfanin da mayakan IS suka kulla inda aka ba kamfanin damar ci gaba da aiki har zuwa 19 ga Satumban 2014.

Kuma tun 2013 kamfanin ke ci gaba da aikinsa duk da yakin da ake yi a Syria.

Kungiyar IS ce dai ke rike da ikon garuruwa da hanyoyin da ke kusa da kamfanin a cewar jaridar Le monde, kuma kamfanin ya samu lasisi tare da biyan kudaden haraji ga mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.