Isa ga babban shafi
Colombia

Majalisar Dinkin Duniya zata tura tawagar sa ido kasar Colombia

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura wata tawagar masu sa ido zuwa kasar Colombia domin taimakawa kasar dawo da tabbataccen zaman lafiya a kasar tsakanin 'yan tawaye da gwamnati

'Yan tawayen FARC sun ajiye makamai
'Yan tawayen FARC sun ajiye makamai Reuters/John Vizcaino
Talla

Tawagar mai kunshe da jami’ai 450 zata shafe shekara guda a kasar Colombian domin sa ido kan mutunta yarjejeniya tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen FARC a yankuna 40 da ke fadin kasar.

Mafi yawancin wadanda ke cikin tawagar ta Majalisar Dinkin Duniyar sun fito ne daga kasashen kudancin Amurka.

Ana sa ran sanya hannu kan yarejejeniya ta karshe da zata kawo karshen fada tsakanin gwamnatin Colombian da ‘yan tawaye a ranar 26 ga Satumba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.