Isa ga babban shafi
Brazil

Lula zai gurfana gaban kotu kan badakalar cin hanci

Kotu ta yanke hukuncin cewar za’a tuhumi tsohon shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva da laifin cin hanci da rashawa, bayan masu gabatar da kara sun zarge shi da almundahana a kamfanin man kasar.

Tsohon shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva zai bayyana gaban Kotu kan zargin rashawa.
Tsohon shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva zai bayyana gaban Kotu kan zargin rashawa. Fuente: Reuters.
Talla

Alkalin kotun Sergio Moro, ya amince da bukatar da masu shigar da kara suka yi na tuhumar tsohon shugaban, wadda zata zama shari’a irin ta ta farko da aka tuhumi manyan yan kasuwa da yan siyasar kasar ta Brazil

Ana dai zargin Lula ne da karbar sama da Dala biliyan daya da miliyan dari a matsayin cin hanci tare da gina wani gida na kasaita a bakin teku.

Tsohon shugaban mai shekaru 70 dai yayi watsi da zargin inda yace hakan ba zai hanashi bayyana ra’ayinsa na siyasa ba.

Sai dai in har kotu ta same shi da aikata laiffukan da ake zarginsa toh hakan zai kawo cikas ga burinsa na sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za’a gudanar a shekarar 2018.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.