Isa ga babban shafi
Faransa

An sake bude hasumiyar Eiffel mai tarihi da ke Paris

An sake bude harabar Tour Eiffel da ke birnin Paris domin bai wa masu yawan bude ido damar yin ziyara, bayan yajin aikin kwanaki biyar da ma’aikata suka yi, tare da rufe wannan hasumiya da ke samar wa Faransa milyoyin kudade daga masu yawon shakatawa.

Hasumiyar Eiffel mai tarihi da ke babban birnin Faransa, Paris
Hasumiyar Eiffel mai tarihi da ke babban birnin Faransa, Paris AFP/Philippe Lopez
Talla

An dakatar da yajin aikin ne, bayan da ma’aikata suka jefa kuri’ar amincewa da hakan, yayin da ake kyautata zaton masu yawon bude ido sama da 20,000 za su ziyarci hasumiyar, domin gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara a karshen wannan wata.

Ma’aikatan dai sun shiga wannan yajin aiki ne rashin amincewa da yadda hukumar gudanarwa ta Tour Eiffel ta kebe kanta ba tare da sauraran shawarwarinsu ba, lamarin da suka ce zai iya kawo cikas ga wannan wuri mai cike da tarihi da aka gina tun a shekara ta1889.

Akalla dai mutane milyan 6 ne ke ziyartar wannan hasumiya a kowace shekara, yayin da a watan Disamba na kowace shekara, ake samun baki masu yawon bude ido akalla 6,000 a rana guda, kuma kashi 80% daga wasu kasashen suke zuwa.

A tsawon kwanaki biyar na yajin aikin, mafi yawa daga cikin bakin da ke ziyartar Tour Eiffel sun kasance ba tare da masu yi musu jagora ba, yayin da wasu sassa suka kasance a rufe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.