Isa ga babban shafi
Jamus

An kashe mutane 12 a kasuwar Kirismati a Jamus

Akalla mutune 12 ne suka rasa rayukansu bayan wata katuwar mota ta afka kan mai-uwa-da-wabi a daidai lokacin da jama’a ke siyayyar kayayyakkin bikin Kirismati a wata kasuwa da ke birnin Baerlin na Jamus.

Kasuwar Kiristamatin da aka kai harin katuwar mota a birnin Berln na Jamus
Kasuwar Kiristamatin da aka kai harin katuwar mota a birnin Berln na Jamus REUTERS/Pawel Kopczynski
Talla

Jami’an ‘yan sanda sun zargi cewa, an kai harin ne da gangan, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane kimanin 50.

Wata majiyar tsaro ta ce, direban motar dan asalin Pakistan ne ko kuma Afghanistan da ya yi gudun hijira a cikin watan Fabarairu.

Yanzu haka dai ana gudanar da bincike don gano alakar lamarin da ayyukan ta’addanci.

Jami’an tsaro sun shawarci mazauna yankin da su zauna a gidajensu saboda tsaro, yayin da aka aike da motocin bada agajin gaggauwa don taimaka wa wadanda lamarin ya ritsa da su.

A ranar 14 ga watan Julin da ya gabata ne, kungiyar IS ta yi amfani da katuwar motar dakon kaya wajen kaddamar da hari kan jama’ar da ke bikin ranar jamhuriyya a birnin Nice na Faransa, in da ta kashe mutane 86.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.