Isa ga babban shafi
Jamus

'Yan sanda na farautar maharin kasuwar Kirismati

Jami'an 'yan sandan Jamus na ci gaba da farautar direbar motar da ta afka wa jama'a da ke cin kasuwar Kirismati  a birnin Berlin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 baya ga wadanda suka raunana. 

Jami'an tsaron Jamus na farautar maharin kasuwar Kirismati da ke birnin Berlin
Jami'an tsaron Jamus na farautar maharin kasuwar Kirismati da ke birnin Berlin REUTERS/Christian Mang
Talla

Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da harin, amma ba ta bada hujja a kan ikirarinta ba.

Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maizierre ya ce, mutumin da ake zargi da kai farmakin ya tsere kuma jami’an tsaro na farautar sa a yanzu, ya yin da aka saki wani dan asalin kasar Pakistan da aka kama bayan aukuwar lamarin, amma daga bisani bincike ya nuna cewa, ba shi da hannu.

Kungiyar IS ta sanar cewar wani sojanta ne ya kai harin a matsayin martani ga hadakar kasashen da ke yaki da mujahidai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.