Isa ga babban shafi
Jamus

Harin Jamus: Za a bada tukuicin Euro dubu 100

Hukumomin Jamus sun yi tayin bada Euro dubu 100 ga duk wanda ya  ba su bayanai har suka cafke Amis Amri, dan asalin kasar Tunusia da ake zargi da kashe mutane 12 a lokacin da ya tuka motar da ta afka kan masu cin kasuwar kirsimeti a birnin Berlin.

Anis Amri da ake zargi da kai farmaki a kasuwar birnin Berlin da ke Jamus
Anis Amri da ake zargi da kai farmaki a kasuwar birnin Berlin da ke Jamus 路透社
Talla

Bayanai sun ce, Amri mai shekaru 23 na da matukar hadari kuma ana zaton yana dauke da makami, saboda haka mutane su yi taka-tsan-tsan, yayin da ake ci gaba da farautar sa.

Hukumomin sun ce, matashin ya yi zaman kaso na shekaru 4 a Italiya kafin ya shiga kasar ta Jamus saboda samun sa da laifin cinna wuta a wani gini.

An dai bayar da umarnin cafke matashin ne bayan jami’an tsaro sun tsinci takardar shaidar zamansa a Jamus a cikin motar da aka yi amfani da ita wajen kai farmakin.

Tuni dai shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta gana da hukumomin tsaro don tattaunawa game da bincike kan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.