Faransa ta kai kamfanin Lafarge kotu
Gwamnatin Faransa ta maka wani katafaren kamfanin kasar Lafarge a gaban kotu, kan laifin kin dakatar da aikin hakar siminti da ya yi a kasar Syria, duk kuwa da bukatar haramcin da kungiyar Tarayyar Turai ta yi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ofishin ministan kudin Faransa ne, ya sanar da daukar wannan mataki na shigar da karar kamfanin a gaban wata kotun da ke birnin Paris.
Wata majiyar shari’a ta ce mai shigar da karar gwamnatin kasar ne, a cikin watan Oktoba ya buda soma binciken, dangane da zargin da ake yi wa katafaren kamfanin na Lafarge da ke aikin hakar simintin al’amarin da a yau ya kai shi ga shigar da karar a gaban kotu.
Ci gaba da gudanar da aikin da kamfanin hakar simintin ya yi a Jalabiya, a arewacin kasar Syria, karkashin wani reshen kamfanin na lafarge a yanki, ya haifar da kace nace a jaridar le Monde da ta bankado lamarin a watan Yunin bara, inda ta zargi kamfanin da ci gaba da gudanar da ayyukin hakar simintin a lokacin da ake cikin yaki a Syria, da cewa ya faru ne karkashin yarjejeniya da ya cimma da kungiyar mayakan jihadi ta IS a yankin.
Karar da ma’aikatar tattalin arzikin Faransa ta shigar dai, da ta shafi haramcin hana sayen man fetur din kasar ta Syria, da kungiyar Tarayyar Turai ta saka a 2012, karkashin jerin takunkuman da ta kakabawa gwamnatin shugaba Bachar Al-Assad.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu