Isa ga babban shafi
Faransa

Batun Tattalin arziki zai mamaye Kamfen a zaben Faransa

Batun Tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga Faransawa da kuma manufofin kasar a kungiyar Tarayyar Turai ne za su mamaye yakin neman zaben ‘yan takarar shugaban kasa da za a gudanar a watan Afrilu.

François Fillon da  Benoît Hamon 'Yan takarar shugaban kasa a zaben Faransa na 2017
François Fillon da Benoît Hamon 'Yan takarar shugaban kasa a zaben Faransa na 2017 REUTERS/Pierre Constant/Pool/Philippe Wojazer
Talla

Adadin marasa ayyukan yi a Faransa ya kai kashi 10 na al’ummar kasar, kuma rashin magance matsalar ya dushe farin jinin shugaba Francois Hollande.

Hollande ya yi alkwarin cewar muddin ya kasa magance matsalar rashin aikin yi ba zai nemi wa’adi na biyu ba.

Yanzu ‘Yan takara 12 ne ke neman kujerar shugaban kasa da suka hada da tsohon Firaminista Francois Fillon da Republican da Marine Le Pen ta jam’iyyar ‘yan kishin kasa (FN) da Emmanuel Macron ministan tattalin arziki a gwamnatin Hollande da kuma Benoit Harmon dan majalisa da ya fice gwamnatin shugaba Hollande.

Matsalar tsaro sakamakon kwararar baki da kuma harin ta’addanci na daga cikin abinda ‘yan takara irin su Marine Le Pen ke cewa ya dace a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a don ficewa daga kungiyar kasashen Turai.

Hasashe ya nuna Le pen za ta kai zagaye na biyu amma za ta sha kaye a hannun Emmanual Macron ko kuma Francois Fillon.

Kodayake farin jin Fillon ya dushe sakamakon zarginsa da azurta iyalin shi ta hanyar biyansu kudaden albashi a lokacin da yana Firaminista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.