Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta fara aiwatar da shirin biyan 'yan gudun hijira kudade

Gwamnatin Jamus ta fara aiwatar da wani shiri, na biyan ‘yan gudun hijira masu neman mafaka a kasar domin komawa kasashensu.

Wasu 'yan gudun hijira a nahiyar Turai
Wasu 'yan gudun hijira a nahiyar Turai
Talla

Karkashin tsarin gwamnati zata biya ‘yan gudun hijira da suka zabi komawa gida bisa ra’ayin kansu kudade, musamman idan sun yi hakan, kafin neman izinin samun mafaka a kasar.

Sai dai kuma, shirin ya ware wani kashi daga cikin ‘yan gudun hijirar da gwamnatin Jamus ta ce basa cikin shirin, wadanda suka kunshi kasashen yankin Balkan da ke gabashin turai, da kuna 'yan gudun hijira daga Syria.

Ma’aikatar lura da bakin haure da kuma ‘yan gudun hijira ta Jamus, tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM, suka kafa sabon tsarin mai suna “StartHilfe Plus”, tare da ware euro miliyan 40 domin aiwatar da shi.

Karkashin tsarin, gwamnatin Jamus zata biya duk wani dan gudun hijira da ya janye bukatar neman mafaka a kasar bisa radin kansa, euro 1,200, don komawa gida, yayinda ‘yan gudun hijirar da aka yi watsi da bukatarsu ta neman mafaka zasu sami euro 800, amma bisa sharadin ba zasu daukaka kara ba a kotu.

Sai dai kuma ‘a gefe guda masu adawa da sabon tsarin a kasar, sun ce hakan wani yunkuri na tauye hakkin ‘yan gudun hijirar da gwamnatin Jamus ke yi, ta hanyar dakile damarsu ta daukaka kara a kotuna, don samun mafaka a kasar, idan gwamnati ta yi watsi da bukatar.

Zuwa yanzu dai akalla ‘yan gudun hijira 430,000 ne suka gabatar da bukatar samun mafaka a Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.