Isa ga babban shafi
Romania

Romania ta soke dokar rashawa da ta janyo zanga-zanga

Gwamnatin Romania ta soke wata ayar dokar cin hanci da rashawa da ta janyo gagarumar zanga-zanga mafi girma a tarihin kasar tun faduwar gwamnatin Nicolae Ceausescu a 1989.

Kwanaki shida aka shafe ana gudanar da zanga-zangar a Romania.
Kwanaki shida aka shafe ana gudanar da zanga-zangar a Romania. Inquam Photos/Octav Ganea
Talla

Gwamnati ta soke dokar ne da ta kunshi wanke jami’an gwamnati daga laifin rashawa da bai zarce darajar kudi kasa da dala dubu 50 ba.

Wannan ne kuma ya harzuka ‘yan kasar suka bazama saman titi suna zanga-zangar adawa da dokar da suke ganin karan tsaye ne ga yaki da cin hanci da rashawa a Romania.

Sai dai kuma har yanzu al’ummar kasar na zanga-zanga a Bucharest duk da gwamnati ta sanar da soke dokar.

Kwanaki shida aka shafe ana gudanar da zanga-zangar a Romania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.