Isa ga babban shafi
Faransa

Dan takarar shugabancin Faransa François Fillon ya nemi afuwa

Dan takarar shugabancin kasar Faransa François Fillon ya nemi afuwa game da daukar matarsa da yayi aiki a matsayin mai taimaka masa.

Dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam`iyyar Republican Francoise Fillon
Dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam`iyyar Republican Francoise Fillon Philippe Wojazer/AFP/Getty Images
Talla

Sai dai kuma tsohon Firaministan Faransar, ya musanta zargin da ake masa na cewa, ya biya matar tasa albashi mai tsoka a bisa aikin da bata gudanar ba.

Tun da fari dai an zargi François Fillon da biyan euro 680,000 a matsayin albashi ga matarsa, yayinda kuma ya dauki `ya`yansa guda biyu aiki inda yake biyan kowanne daga cikinsu euro 84,000 a matsayin albashi, daga cikin kudin `yan majalisar kasar Faransa a tsakanin shekarun 2005 da 2007.

To sai dai kuma Fillon ya kare kansa da cewa, daukar `ya`yansa da yayi ai bai sabawa dokar ba, illa dai aikata irin haka daga shugabanni irinsa kan haifar da zargi tsakaninsu da al`ummah kamar yadda ya faru yanzu.

Wani abin da kuma ya dauki hankali kan wannan danbarwa da Fillon dake takarar shugabancin Faransa karkashin jam`iyyar Republican shi ne yadda yayi watsi da kira kirayen da ake masa na ya janye takarar da ya ke ta neman shugabancin Faransa, inda ya ce ai yanzu ma zai kaddamar da wani sabon yakin neman zaben.

Kafin bayyanar wannan zargi da Fillon ke fuskanta, sati biyu da suka gabata, kuri`ar jin ra`ayin jama`a ta nuna ya zarta abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen farinjini, amma a halin yanzu lamarin ya sauya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.