Isa ga babban shafi
Faransa

Fillon na zargin wasu da yi masa zagon-kasa

Dan takaran shugabancin kasar Faransa Francois Fillon ya yi zargin cewar wasu na neman raba shi da tikitin takarar da ya samu sakamakon zarge- zargen da ake yi wa matarsa na karbar kudade ba tare da yin wani aiki ba.

Francois Fillon da ke neman shugabancin Faransa a zabe mai zuwa, na cikin tsaka mai wuya
Francois Fillon da ke neman shugabancin Faransa a zabe mai zuwa, na cikin tsaka mai wuya REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

A jiya wata kafar yada labarai ta yada wata hirar da akayi da matar Fillon, wato Penelope shekaru goma da suka wuce, in da ta ke cewa ba ta taba yi wa mijinta aiki a  matsayin mataimakiya ba.

Jaridar Le parisien ta bayyana cewa, a wata hira da jaridar The Sunday Telegraph ta kasar Birtaniya ta yi da ita, a game da yadda take tafiyar da al’amuranta a lokacin da mijinta ya dare mukamin Firaministan Fransa, in da ta ke cewa takan halarci tarukan siyasa amma takan zabi ta koma kujerar baya don sauraran jawaban da ake yi.

Sai dai wannan ba shi bane illar, illa wasu jimloli biyu da ta yi amfani da su a lokacin hirar da jaridar The Sunday Telegraph, in da ta ke cewa, bata taba zama maitakaimakiya ko kuma sakatariyar yada labaran minjinta ba, a hirar da da aka yi da ita a shekarar 2007.

Sai dai duk da haka uwargida Penelope Fillon ta share tsawon shekaru 4 tana karbar albashin Euro dubu 5 a matsayin mai taimaka wa mijinta kan harkokin majalisa daga shekarar 1998 zuwa 2002.

Al’amarin da jaridar Le Parisien ta gabatar a matsayin abin dubawa na zama ma’akaciyar bogi da ke karbar albashi ba tare da kasancewa ma’aikaciya ba, lura da kalaman nata a jaridar The Sunday Telegraph.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.