Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na fuskantar tirjiya a zaben ministoci

Shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar kalubale a Majalisar dattijan Amurka wajen tantance ministocinsa wadanda ya gabatar da za su tafiyar da gwamnatin shi.

An nada Jeff Sessions a kan mukamin ministan shari'a a Amurka
An nada Jeff Sessions a kan mukamin ministan shari'a a Amurka REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

Da kyar dai Majalisar Dattijan ta amince da Jeff Sessions a matsayin ministan shari’a bayan samun rarrabuwa kanun ‘yan majalisa musanman jam’iyyar Democrat da suka ki amincewa a tabbatar da shi.

Ana zargin Sessions da nuna wariyar launin fata duk da cewa ya musanta hakan.

Sai kuma Betsy DeVos da Trump ya nada a matsayin Sakatariyar harakokin kula da ilimi, da ita ma da kyar ta samu amincewar Majalisa saboda kasancewarta ‘yar jari hujja inda a rayuwarta ba ta taba cin moriyar makarantun gwamnati ba sai na kudi.
Sai da aka shafe sa’o’I 24 ana tabka muharawa a Majalisar datitjan Amurka Kafin tantance Betsy Devos, a matsayin sakatariyar kula da harakokin ilimi a Gwamnatin Trump.

Devos ta fuskanci adawa daga baganren ‘Yan democtrat a Majalisa da kuma wasu ‘Yan Republican da suke ganin ba ta cancanci ta jagoraci hrakokin ilimin Amurka ba saboda manufofinta ga ilimi da kuma yadda bata taba rike wani mukamin gwamnati ba.

Sai da dai mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya shiga tsakanin kafin ta samu amincewar Majalisa.

Devos ta taba fuskantar bore a kan wani toskaci da ta yi cewa makarantu na bukatar bindiga domin kare kansu.

Yanzu dai tana cikin ministoci 6 da suka samu amincewar Majalisa kuma Babban kalubalen da ke gabanta shi yadda zata tafiyar da ilimi ba tare da tana da kwarewar aikin gwamnati ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.