Isa ga babban shafi
Faransa

Tsugune bata karewa dan takarar shugabancin Faransa ba François Fillon

Masu gabatar da kara a Faransa sun bayyana cewa zasu dauki mataki na gaba na cigaba da bincikar zargin da ake wa dan takarar shugabancin Faransa, François Fillon na aikata ba dai dai ba.

Dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar republican François Fillon yayin ziyarar da ya kai tsibirin Réunion.
Dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar republican François Fillon yayin ziyarar da ya kai tsibirin Réunion. REUTERS/Laurent Capmas
Talla

Ana zargin Fillon da ke takara a karkashin Jam’iyyar Republican, da dauka tare da biyan matarsa Penelope Fillon, albashin da ba ta yi aikin da ta cancanci a biyata ba, a lokacin da ya ke rike da Firaminista kasar, zargin da yake cigaba da musantawa da cewar tabbas matar tasa ta gudanar da aikinta kamar yadda doka ta tanadar

Ba da dadewa ba ne, lauyoyin Fillon suka kalubalanci lauyoyin gwamnati da cewa basu da wata cikakkiyar shaida bisa zargin da ake yiwa dan takarar.

Sai dai lauyoyin gwamnati sun ce zasu cigaba da gudanar da bincike kan zargin.

Yayin wata ziyara da ya kai zuwa tsibirin Reunion, Fillon ya shaidawa magoya bayansa cewa, zai cigaba da taka takarar neman shugabancin kasar har sai yaga abinda zai turewa buzu nadi, duka da suka, da kuma kiraye kirayen ya janye takarasa da yake sha.

François Fillon ya ce yana wannan kafiya ce saboda bukatarsa ta dawo da kima da kuma karfin tattalin arzikin kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.