Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan Jam’iyyar Republican na matsin lamba ga Fillon

Tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon na fuskantar bore daga ‘Yan majalisun Jam’iyyarsa ta Republican wadanda ke matsin lamba ya jingine takararsa sakamakon badakalar da aka bankado game da azurta iyalin shi da kudaden jama’a, lamarin da ya dushe farin jininsa ga Faransawa.

Dan takarar Republican François Fillon a zaben Faransa
Dan takarar Republican François Fillon a zaben Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

‘Yan Republican na ganin Fillon ba zai kai labari ba, kamar yadda kuri’un jin ra’ayin jama’a suka nuna, yayin da shi kuma ya nace ba zai jingine takarar ba saboda kotu bata tabbatar da zargin da ake mashi ba.

Fillon na fuskantar adawa ne daga Gungun ‘Yan Majalisun 40 a jam’iyyarsa ta Republican inda suka gana a jiya kan makomar takarar shi bayan wa’adin da ya ba su na kwanaki 15 ya kawo karshe.

‘Yan majalisun sun hadu ne a gidan wani abinci a Paris inda suka tattauna a game da wanda da ya dace ya tsaya takarar shugaban kasa a Jam’iyyar.

Fargabar ‘yan majalisun dai shi ne yadda hasashe ke tabbatar da jam’iyyarsu ba zata kai labari ba zagen shugaban kasa da za a gudanar a watan Afrilu.

Kuma yanzu sun kira babban taron jam’iyyar domin tattauna makomar takarar Fillon.

Mista Fillon wanda a farko ake ganin zai lashe zaben shugaban kasa, amma yanzu kuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna ba zai kai labari ba bayan bankado zargin ya yi amfani da kudaden kasa domin biyan uwar gidan shi albashi a lokacin da yana Firaminista zamanin mulkin Sarkozy.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.