Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Faransa, Amurka da Japan zasu cigaba da kuntatawa Korea ta Arewa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump, da kuma shugaban Japan Shinzo Abe, sun tattauna ta wayar tarho, dangane da tsaurara takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakabawa Korea ta Arewa.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. Reuters
Talla

A karshen tattaunawar da ta gudana tsakanin shugabannin uku, sun cimma matsayar cigaba da daukar matakan kuntatawa Korea ta Arewan har sai ta bada kai.

A gefe guda kuma Korea ta Kudu na cikin zulumi, a dalilin wasu bayanai da ke nuni da cewa, a kowane lokaci makwabciyarta Korea ta Arewa, zata sake wani gwajin makamin na nukiliya, baya ga wanda ta yi a kwanakin da suka gabata.

A farkon makon daya gabata gwamnatin Korea ta Arewa ta bayyana cewa, ta samu nasara dari bisa dari kan gwajin sabon makamin nukiliyar da tayi, wanda ke kunshe da sinadrin Hydrogen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.