Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai kara kudadden haraji kan manyan kamfanoni

Gwamnatin kasar Faransa ta ce za tayi karin kudadden haraji na wucin-gadi kan manyan kamfanonin kasar, domin cike gibin tattalin arzikinta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Shugaba Emmanuel Macron ya alkawarta kaddamar da tsarin ne domin taimakawa gwamnatinsa cike gibin kasafin kudin kasar kamar yadda dokokin kungiyar tarayyar Turai ya tanadar.

Wannan na zuwa ne bayan biyan harajin kudadden da yawansa ya kai euro biliyan 10 da gwamnatin Francois Hollande ta sanyawa wasu kamfanonni.

A waccan lokacin sai da ‘yan adawa suka kalubalanci matakin, abin da ya kai ga kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar bada umarnin mayarwa kamfanonin kudadensu, wanda hakan ya haifar da babban gibi ga kasafin farko na gwamnatin Macron.

Sabon tsarin na matsayin kashi 2 bisa 3 na euro 15b da gwamnatin kasar tace zata samar nan da shekara mai zuwa.

Tsarin karin kudadden harajin na zuwa ne yayin da wasu manyan kamfanonni kasar da ke yammaci, shirya kai gwamnatin Faransa kotu kan harajin da aka zabtare musu.

Gwamnatin Macron ta kuma sanar da shirin sayar da hannayen jari na kashi 4.73 na kamfanin kera motocin kasar wato Renault, wanda shima ana iya kallonsa a matsayin yunkuri na samar da karin kudade ga gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.