Ana zargin kamfanin Larfarge da yin alaka da ISIS
Kamfanin hada siminti na Lafarge, ya ce jami’an bincike na kasar Faransa, sun kai samame a ofisoshinsa, domin neman bayanai da ke alakanta kamfanin da kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Syria, musamman IS.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun kamfanin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa, ana yin binciken ne domin tantance sahihancin rahoton da wani gidan rediyo ya bayar a kan zargin.
Tun a cikin watan Yuni, wasu alkalai a Faransa, suka fara bincike kan rahoton da ya ce, kamfanin simintin na Lafarge, ya tura kudade ga wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda a Syria, daga cikinsu kuma har da kungiyar IS.
Rahoton ya ce kamfanin ya yi haka ne, domin ya samu damar cigaba da ayyukansa a arewacin kasar ta Syria, duk da irin rikicin da kasar ke fama da shi.
Rahoton da ya bulla a bara, ya ce kudaden da kamfanin simintin ya biya kungiyoyin a Syria kudi sun kama daga dala dubu 80, zuwa dala dubu 100, domin samar da tsaro ga ma’aikatansa a tsakanin shekarun 2013 da 2014, kuma aka rawaito cewa IS ta samu kason dala dubu 20.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu