Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta yi watsi da bukatar Amurka kan Korea ta arewa

Rasha ta yi watsi da bukatar Amurka kan ta yanke hulda da Korea ta arewa, bayan da kasar ta sake yin gwajin makami mai linzami a jiya. Ministan harkokin wajen Rashan Sergey Lavrov ya ce kasarsa na ganin cewa yanke hulda da Koriya ta Arewa mataki ne da ba zai taimaka ta kowane fanni ba.

A cewar ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov yakin cacar-baki da ke wakana tsakanin Amurak da Fadar Pyonyong ya yi kama da wasan yara.
A cewar ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov yakin cacar-baki da ke wakana tsakanin Amurak da Fadar Pyonyong ya yi kama da wasan yara. AFP
Talla

Mr Lavrov da ya ke jawabi kan batun, ya ce Rasha ta sha nanata cewa matsi ko kuma takunkuman da ake sanyawa sun isa, yayinda su ke kallon matakan da Amurka ke dauka a baya-bayan nan a matsayin wani yunkuri na tunzura koriya ta arewar kaddamar da wasu tsauraran matakai.

Lavrov ya kuma zargi Amurka da yunkurin yin amfani da wannan dama wajen ganin ta tarwatsa kasar.

Mr Lavrov ya kafa hujja da wani gagarumin atisayin soji da Amurka ke shirin gudanarwa tare da hadin guiwar koriya ta kudu a cikin watan Disamba, wanda ya ce hakan wani salo ne na takala, a maimakon haka, a cewarsa, kamata ya yi Amurka ta bi hanyar zama kan teburin shawarwari.

Saboda haka, ministan ya ce akwai bukatar Amurka ta fito fili ta bayyana idan har ta na so ne ta yi wa kasar ta koriya ta arewa hawan kawara, matukar dai manufar tata ke nan.

Ko a cikin watan Satumba dai ministan na harkokin wajen kasar Rasha ya yi kira ga bangarorin masu gaba da juna game da maganar ta kasar koriya ta arewa da su sassauta, domin a cewarsa yakin cacar-baki da ke wakana tsakanin Amurak da Fadar Pyonyong ya yi kama da wasan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.