Isa ga babban shafi
Turai

Ƙasashen Turai sun cimma jituwa kan yaki da ta'addanci

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sanar da cimma jituwa a tsakanin ƙasashe mambobinta domin yin musayar bayanai da za su taimaka domin tantance jama’a da kuma yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.

Jami'an tsaron Trurai za su rika musayar bayanan sirri a ƙarkashin sabo tsarin yaki da ta'addanci a nahiyar
Jami'an tsaron Trurai za su rika musayar bayanan sirri a ƙarkashin sabo tsarin yaki da ta'addanci a nahiyar Ronny HARTMANN / AFP
Talla

A ƙarkashin sabuwar yarjejeniyar, ƙasashen yankin za su rika yin musayar bayanai akan matafiya domin tantance waɗanda za su iya kasancewa barazana ga sha’anin tsaronsu.

Har ila yau sabon shirin zai bai wa ƴan sanda damar isa ga sauran bayanan sirri da suka jiɓanci wanda ake zargi, kamar dai yadda kwamishinan tsaro na kungiyar Julian King ya sanar jim kaɗan bayan kammala wani taro a birnin Strasbourg da ke gabashin Faransa.

Hakan dai na nufin cewa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro na da damar isa ga bayanan sirrin da suka shafi ƴan asalin yankin na Turai da ma sauran matafiya, tare da rarraba wadannan bayanai a tsakanin kasashe ba tare da wani shinge ba.

Daga cikin waɗannan bayanai har da alamar yatsa da fuska da kuma sunayen jama’a da ke bayar da damar gano asalin mutum a sauwake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.