Yan aware sun lashe zaben Catalonia
Yan awaren yankin Catalonia a jiya alhamis sun yi nasarar rike rinjayen da suke da shi a majalisar dokokin yankin, al’amarin da ya sake jefa kasar Spain cikin rashin tabbas, tun bayan yukurin yan awaren dake ci gaba da daukar hankali a nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Bayan kirga sama da kashi 99,8% na kuriún zaben da aka kada ne, jamíyun yan aware uku sun kwashe kujeru 70 daga cikin 135 da ake da su a majalisar dokokin yankin na Catalonia.
Tsohon shugaban yankin mai gudun hijira a Bruxos Carles Puigdemont ya bayyana matukar farin cikin sa da cewa yanzu kam yar fage ta nuna, gwamnatin Spain ta kasa a guiwa.
Sakamakon zaben bamai kyau bane ga firaministan Spain Mariano Rajoy wanda ya kasa sanyaya guiwar yan awaren, da suka kalubalance shi a zaben .
Jam’íyyar shugaban gwamnatin Spain ta rasa gurbin kujeru 8 daga cikin 11 da takeda su a majalisar ta Catalonia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu