Isa ga babban shafi
Amurka-Trump

Cohen ya sharara karya don neman sassauci a hukunci- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa tsohon lauyansa Michael Cohen ya sharara karya ne gaban kotu don neman sassauci hukuncin da za a yanke masa, dalili kenan da ya amsa ya yiwa zaman Majalisun kasar karya kan kutsen Rasha a zaben kasar da ma kwangilar ginin rukunin gidaje Real Estate.

Trump wanda ya ke bayanin gabanin tafiya taron G20 da ke gudana a Argentina ya ce dama can Cohen mutum ne mai rauni dalili kenan da ya sanya shi sharara karya.
Trump wanda ya ke bayanin gabanin tafiya taron G20 da ke gudana a Argentina ya ce dama can Cohen mutum ne mai rauni dalili kenan da ya sanya shi sharara karya. Reuters
Talla

Kalaman na Trump wanda ke zuwa bayan Micheal Cohen ya amsa laifin yin karya gaban zaman majalisun dokokin kasar yayin gurfanar da ya yi gaban kotu jiya Alhamis ya ce dama Cohen mutum ne mai matukar rauni.

A cewar Trump Micheal Cohen na da tun fil azal na da raunin gaske dalili kenan da ya sanya shi sharara karyar kan abin da kowa ya san gaskiyarsa don samun rangwame, inda ya nanata cewa babu gaskiya a batun da Cohen ke amincewa da shugaban na da masaniya a kusten Rasha cikin zaben kasar na 2016.

Yayin tuhumar da ake yiwa Cohen gaban Kotu, kai tsaye tsohon lauyan na Donald Trump ya amsa cewa ya bayar da sanarwar bogi kan tuhumar kwangilar ginin gidaje ta Real Estate baya ga amsa cewa tawagar masu yakin neman zaben Trump ta gana da wasu wakilan Rasha a ginin Trump Tower wanda ya kai ga tattauna batun kutse a zaben kasar.

Cohen ya amsa cewa ya bayar da bayanan karya kan batutuwan biyu wadanda kai tsaye suka yi yawo da hankalin shari’a baya ga kin bayyana gaskiya gaban zaman majalisun kasar a Newyork.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.