Isa ga babban shafi
Birtaniya

May ta tsallake kuri'ar yankar kauna a Birtaniya

Firaministar Birtaniya Theresa May ta tsallake rijiya da baya a kuri’ar yankar kaunar da ‘yan Majalisar kasar suka kada dangane da kiki-kakar yarjejeniyar ficewar kasar daga gungun kasashen Turai.

Uwargida Theresa May a gaban Majalisar Dokokin Birtaniya
Uwargida Theresa May a gaban Majalisar Dokokin Birtaniya Reuters TV via REUTERS
Talla

Kada kuri’ar yankar kaunar na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ‘yan makwanni Birtaniya ta kammala ficewa daga kungiyar kaasashen Turai.

A karon farko kenan cikin shekaru 26 da Majalisar Birtaniya ke kada irin wannan kuri'ar yankar kaunar a tarihin siyasar Birtaniya, in da Uwargida May ta samu kuri’u 325, wanda ya zarce na ‘yan adawa masu kuri’u 306.

Sai dai ana ganin bangaren jam’iyyar adawa zai ci gaba da kokarin ganin ya kawar da gwamnatin May ta hanyar tinzira gudanar da zaben gama-gari cikin gaggawa kafin ranar 29 ga watan Maris, lokacin da ake sa ran Birtaniyar ta raba gari baki daya da Turai.

A halin yanzu dai, May ta yi alkawarin komawa zauren Majalisar Birtaniya a ranar Litinin mai zuwa, in da za ta gabatar da wani sabon tsarin cimma yarjejeniyar ficeawar.

Da dama daga cikin jami’an diflomasiyar Turai na ganin cewa, watakila a jinkirta batun ficewar Birtaniya domin kauce wa sake fada wa cikin wani rudanin cimma matsaya tsakanin bangarotin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.