Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Majalisar Birtaniya ta amince da tsawaita wa'adin ficewa daga EU

‘Yan Majalisun Birtaniya sun yi watsi da batun sake kada kuri’ar ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai yayinda a bangare guda kuma suka kada kuri’ar amincewa da tsawaita lokacin ficewar kasar daga EU sabanin wa’adin farko na 29 ga watan Maris.

Majalisar Birtaniya yayin zaman kada kuri'ar a yau Alhamis
Majalisar Birtaniya yayin zaman kada kuri'ar a yau Alhamis Reuters TV via REUTERS
Talla

Galibin ‘yan Majalisun na Birtaniya sun kada kuri’ar amincewa da tsawaita wa’adin ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai, zuwa nan da watan Yunin shekarar nan inda suka nemi Firaminista Theresa ta sake garzawa gaban kungiyar ta EU don neman izinin kara wa’adin.

Yayin zaman majalisar na daren jiya Alhamis, ‘yan Majalisun birtaniya 412 ne suka amince da batun tsawaita wa’adin ficewar daga EU, yayinda ‘yan Majalisu 202 suka ki amincewa da batun.

A bangare guda dangane da batun, sake kada kuri’ar ficewar kasar daga EU, ‘yan majalisu 334 ne suka kalubalanci matakin yayinda ‘yan majalisu 85 suka amince da shi.

Bisa wa’adin farko dai dududu, makwanni biyu ya ragewa Birtaniyar ta fice daga EU, dai dai lokacin da Majalisar kasar har sau biyu ta yi watsi da yarjejeniyar ficewar kasar da Theresa May ta cimma da shugabannin EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.