Tsananin zafi ya tilasta rufe makarantu dubu 4 a Faransa
Faransa ta fuskanci yanayi mafi zafi cikin shekaru sama da 10 a karshen makon nan, bayanda matakin zafin a ma’aunin Celsius ya kai digiri 44.3 a sassan kasar.
Wallafawa ranar:
Tuni dai aka samu rahotannin hasarar rayuka a sassan nahiyar Turai, a dalilin yanayin zafin da ke daga tsananta.
Faransa, Spain, Italiya da kuma wasu yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Turan iftila’in tsananin zafin yafi shafa.
Akalla makarantu dubu 4000 aka rufe a sassan Faransa don kaucewa zafin, gudun sake fuskantar rasa rayukan da aka yi a kasar cikin shekarar 2003, inda akalla mutane dubu 15 suka halaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu