Isa ga babban shafi
Rasha

An dirka wa jagoran 'yan adawan Rasha guba

Likita da kuma lauyan jagoran ‘yan adawar Rasha, Alexie Navalny, sun ce an sanya wa shugaban 'yan adawan guba, yayinda aka mayar da shi kurkuku ba tare da yin la’akari da halin da yake ciki ba.

Jagoran 'yan adawan Rasha Alexie Navalny a hannun jami'an 'yan sandan kasar.
Jagoran 'yan adawan Rasha Alexie Navalny a hannun jami'an 'yan sandan kasar. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

A ranar Lahadi ne aka yi gaggawar garzayawa da Navalny asibiti bayan da idanunsa suka kumbura tare da zubda ruwa, sai kuma kurajen da suka bayyana a wasu sassan jikinsa, kamar yadda likitarsa Anastasia Vasilyeva ta shaida wa manema labarai, tare da karin bayanin cewa wata guba da ba ta tantance ko wacce iri bace ta haifar masa da rashin lafiyar.

Likitar jagoran 'yan adawan ta kuma zargi jami’an lafiyar da suka duba Navalny da kokarin rufe gaskiyar abinda ya same shi da gangan ta hanyar gaggauta maida shi gidan yari, inda ta yi zargin an ajiye shi a muhalli mara kyau.

Tun a makon da ya gabata jami’an tsaron Rasha ke tsare da Navalny a gidan yari, bayan ya bukaci a gudanar da zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin kasar na haramtawa wasu ‘yan takara masu zaman kansu shiga zaben ‘yan majalisar kasar da za a yi a watan Satumba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.