Isa ga babban shafi
Amurka - Afghanistan

Duk wanda ya cutar da Amurka zai gamu da zazzafar martani - Biden

Shugaba Joe Biden na Amurka ya kare matakin da ya dauka na janye illahirin sojojin kasar daga Afghanistan, duk da cewa yana shan kakkausar suka dangane da ficewar dakarun kasar a daidai lokacin da ake tsakiyar aikin kwashe jama’a daga birnin Kabul.

Joe Biden shugaban Amurka.
Joe Biden shugaban Amurka. AP - Evan Vucci
Talla

Joe Biden ya ce a lokacin da yake yakin neman zaben shugabancin Amurka, ya fito karara ya shaida wa duniya cewa zai kawo karshen yakin da kasar ke yi a Afghanistan, saboda hakan ya zama wajibi ya cika wannan alkawari ta hanyar janye dakarun baki daya.

Biden, wanda ke gabatar da jawabi kasa da sa-o-i 24 da ficewar dakarun Amurka daga Afghanistan, ya ce sam ba ya nadama a game da wannan mataki da ya dauka, yana mai cewa babbar manufar kaddamar da yakin ita ce tabbatar da cewa Afghanistan ba ta zama maboyar da ‘yan ta’adda za su yi amfani da ita don yi wa Amurka illa ba.

To sai dai shugaba Biden ya ce janyewar ba wai tana nufin cewa Amurka ta kawo karshen yaki da ayyukan ta’addanci ba ne a duniya, yana mai gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin cutar da kasar, to lalle kuwa zai fuskanci zazzafan martatani.

A wani bangare na jawabinsa, shugaba Joe Biden ya ce zai tabbatar da cewa an kwashe sauran Amurkawa da suka makale a birnin Kabul, wadanda aka bayyana cewa adadinsu zai kai 200, tare da ci gaba da karfafa hanyoyin diflomasiyya don fayyace makomar alaka tsakanin Amurka da Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.