Isa ga babban shafi
Jamus-Corona

Wani Magidanci ya kashe kansa da iyalansa bayan amfani shaidar rigakafi ta bogi

Hukumomin kasar Jamus sun ce wani dan kasar ya kashe matar sa da ‘ya'yansa guda 3, kafin daga bisani ya kashe kan sa saboda kaucewa zuwa gidan yari sakamakon amfani da shaidar karbar rigakafin corona na bogi.

Kasashe na amfani da shaidar rigakafin na Covid-19 gabanin baiwa jama'a damar cudanya cikin mutane don dakile yaduwar cutar.
Kasashe na amfani da shaidar rigakafin na Covid-19 gabanin baiwa jama'a damar cudanya cikin mutane don dakile yaduwar cutar. AP - Andrew Medichini
Talla

Mai gabatar da kara a Brandenburg ya ce an samu gawarwakin mutanen 5 a gidansu da ke Koenigs Wuterhausen a wajen Birnin Berlin tare da sakon da mutumin ya rubuta akan dalilin kashe iyalan na sa.

Mutumin mai shekaru 40 ya bayyana cewar ya samarwa matara sa shaidar rigakafin na bogi, yayinda shugaban wurin da ta ke aiki ya gano shaidar, ya kuma bayyana shirin gudanar da bincike akan lamarin.

Mai magana da yawun ofishin mai gabatar da kara Gernot Bantleon ya ce mutumin na fargaba cewar za a daure shi tare da matarsa, yayin da kuma za a kwace ‘ya'yan su.

Masu binciken sun ce mutumin ya kashe yaran na sa masu shekaru 4 da 8 da kuma 10, tare da matar mai shekaru 40, kafin kashe kann sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.