Isa ga babban shafi
Faransa-Ilimi

Malaman makarantu a Faransa sun bukaci murabus din ministan ilmi

Ministan ilimin Faransa ya na fuskantar kiraye-kirayen yin murabus sakamakon wani yawon shakatawa da ya je kasar Spain, inda daga nan ne ya sanar da tsauraran matakan gwajin cutar Covid-19 ga dalibai, lamarin da ya janyo caccaka daga malamansu.

Ministan ilimin Faransa, Jean-Michel Blanquer.
Ministan ilimin Faransa, Jean-Michel Blanquer. © RFI
Talla

Jean-Michel Blanquer, wanda na hannun daman shugaba Emmanuela Macron ne ya kaddamar da sabbin dokokin gwajin cutar Covid-19 da killacewa a wata ganawa ta kafar bidiyo da ya yi da jaridar Parisien a ranar 2 gawatan Janairu, sa’o’i kafin a bude makarantu da ke hutu a lokacin.

Jaridar ba ta fayyace ko Blanquer, wanda ya harzuka malaman makaranta da sauye sauyen da ya yi wa dokokin kariya daga cutar korona, har suka yi yaji aiki a makon da ya gaba, yana magana ne daga wajen shakatawa na tsibirin Ibiza a kasar Spain ba, ganin yadda hotunan da ta dauka suka nuno shi tamkar yana cikin ofishinsa ne.

Sabbin dokokin da ya bijiro da su sun tilasta wa dubban dalibai barin ajizuwansu, zuwa dogayen layukan tare da iyayensu a wajen shagunan sayar da magunguna da dakunan gwaji don neman a gwada su.

Blanquer ya shaida wa ‘yan majalisar dokokin kasar a Talatar nan  cewa bai aikata ba daidai ba, sai dai ya yi kuskure wajen yin sanarwar a wajen yawon shakatawa.

Malaman dai sun dage dole sai ministan ya yi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.