Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Faransa na shirin janye dokar tilastawa matafiya gwajin corona

A yayin da ake samun raguwar masu harbuwa da cutar covid19, nan ba da jimawa ba Faransa zata janye dokar dake tilastawa wadanda suka karbi rigakafin cutar covid19 daga Kasashen da basa tarayyar turai, nuna takardar shaidar gwajin tabbatar da basu dauke da cutar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AFP - YOAN VALAT
Talla

Ministan Tarayyar Turai Clement Beaune da ya shaidawa gidan talabijin Faransar cewar nan da kwanaki masu zuwa zasu sanar da janye gudanar da gwaji ga wadanda suka karba allurar rigakafin  cutar ta corona, bayaga bukatar sakamakon gwajegwajen da aka gudanar cikin watan disambar shekarar bara.

A halin yanzu dai ko da shaidar karbar allurar rigakafin, dole duk wanda bai kasance cikin tarayyar turan ba ciki har da Birtaniya, ya nuna shaidar gwaji na kasa da sa’a 48 kafin a bashi damar shiga Kasar.

Beaune ya kara da cewa a cikin wannan mako da yiwuwa a tsara sabuwar dokar da zata shafi mutanen da aka yi wa allurar rigakafin corona, wadanda basa cikin kungiyar ta EU.

Tun a ranar 25 ga watan janairun da ya gabata ne kungiyar tarayyar tuirai tayi yarjejeniyar tsara dokokin tafiye tafiye, musamman ga mutanen dake shige da fice ciki da wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.