Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Tsarin Mulkin Faransa ta amince da dokar tilasta yin rigakafin Korona

Majalisar Tsarin Mulkin Faransa ta amince da sabuwar dokar rigakafin Korona, wadda ta tilastawa mutane masu shekaru 16 zuwa sama nuna shaidar yin allurar rigakafin cutar, kafin shiga wuraren taron jama'a kamar mashaya, gidajen abinci da gidajen Sinima.

Wasu Faransawa yayin zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tilastawa jama'a yin allurar rigakafin Korona a birnin Bayonne, da ke kudu maso yammacin kasar Faransa. 7 ga Agustan shekarar 2021.
Wasu Faransawa yayin zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tilastawa jama'a yin allurar rigakafin Korona a birnin Bayonne, da ke kudu maso yammacin kasar Faransa. 7 ga Agustan shekarar 2021. AP - Bob Edme
Talla

Sabuwar dokar dakile yaduwar annobar ta Korona dai, wani bangare ne na yunkurin shugaba Emmanuel Macron da ya sha alwashin kuntatawa tsirarun mutanen da ba a yi musu allurar rigakafin cutar Koronar ba.

Dokar tilasta nuna shaidar rigakafin Koronar dai, za ta fara aiki ne daga ranar 24 ga Janairu, wadda ta maye gurbin dokar nuna takardar shaidar rigakafin, ko gwajin mutum ba ya dauke da cutar, ko kuma shaidar da ke nuna warkewa daga cutar.

Sai dai Majalisar tsarin mulkin kasar ta Faransa, ta ki amincewa da bukatar gwamnati ta tilastawa masu halartar tarukan Siyasa nuna shaidar karbar  rigakafin na Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.