Isa ga babban shafi
EU - Belarus

EU ta laftawa hafsoshin sojin Belarus 22 takunkumai

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta tsaurara takunkumin karya tattalin arziki kan Belarus tare da sanya sunayen wasu manyan hafsoshin sojin kasar 22 cikin bakin kundinta, sakamakon rawar da Belarus din ke takawa a yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko.
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko. AFP - MAXIM GUCHEK
Talla

Sojojin Rasha sun yi amfani da kasar Belarus a matsayin sansanin harba makamai masu linzami na kasa da ta sama kan makwabciyarta Ukraine.

Sabbin takunkuman da aka kakabawa Belarus sun zo ne bayan laftawa kasar Rasha takunkumai har zagaye uku da suka shafi tattalin arzikinta, da shugabancinta har zuwa ga shugaba Vladimir Putin, da kuma bangaren sufurin jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.