Isa ga babban shafi
Gabashin Turai

NATO ta fara atasaye da dakaru dubu 30 a Norway

Dakarun kungiyar tsaro ta NATO sun fara gudanar da wani gagarumin atisayen soji a kasar Norway.

Tankokin yakin sojojin kasashen kungiyar tsarob ta NATO yayin shirin fara atasaye da sojoji dubu 30 a Norway.
Tankokin yakin sojojin kasashen kungiyar tsarob ta NATO yayin shirin fara atasaye da sojoji dubu 30 a Norway. AFP - GEIR OLSEN
Talla

Atisayen wanda aka yi wa take ‘Cold Response’, dakaru dubu 30 ne za su gudanar da shi daga kasashe 23.

Jiragen yaki na sama kimanin 200 da kuma jiragen yakin ruwa 50 na cikin atasayen sojojin na kasashen kungiyar tsaro ta NATO, wanda zai kai har zuwa ranar 1 ga Afrilu kafin a kammala shi.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da duniya ta shiga zaman dar dar sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, inda take cigaba da kai hare-hare a sassan kasar, domin hana makwafciyar tata  kasancewa mamba a kungiyar tsaro ta NATO, da a yanzu ta kaddamar da atisayen soji.

A karshen makon da ya gabata dai Rasha ta tsananta hare-haren da take kaiwa cikin Ukraine, wannan karo a bangaren arewaci da kuma yammacin kasar, yayin da alkalumma ke cewa mutane 35 sun rasa rayukansu a daya daga cikin hare-haren jiragen yakinta suka kai barikin Lviv kusa da iyakar Ukraine da Poland.

To sai dai a sanarwar da ta fitar, ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kashe sojin haya ‘yan asalin kasashen ketare akalla 180 ne ne a lokacin da suke kokarin shiga Ukraine daga iyakar Poland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.