Isa ga babban shafi

Mashawarcin Biden kan Korona ya kamu da cutar

Babban mashawarcin shugaban Amurka Joe Biden kan yaki da yaduwar cutuka musamman ma Korona, dakta Anthony Fauci ya kamu da cutar.

Dakta Anthony Fauci.
Dakta Anthony Fauci. AFP
Talla

Jami’an lafiya sun ce sakamakon gwajin da aka yi wa  dakta Fauci ne ya tabbatar da cewa babban jami’in ya kamu da annobar a ranar laraba. Sai zai cigaba da gudanar da ayyukansa daga gida  har zuwa lokacin da zai warke sarai.

Cibiyar kula da lafiyar Amurka ta ce kawo yanzu alamu marasa karfi daktan ke fuskanta dangane da cutar ta Korona, zalika akwai tabbacin cewar bai yi wata hulda ta kai tsaye da shugaban Amurka Joe Biden ba, wanda yake a matsayin mashawarcinsa kan sha’anin lafiya.

Kafin kamuwa da annobar ta Korona dai dakta Fauci ya dade da karbar allurar rigakafin cutar ta Korona, zalika sau biyu yana karbar karin rigakafin.

Tun bayan barkewar cutar Korona tare da fantsamar ta zuwa sassan duniya, Fauci ya zama amintaccen jami’in lafiyar da Amurka ta dogara dashi wajen samun bayanai da kuma shawarwarin yadda za a dakile annobar.

Sai dai yadda likitan ya rika tsage gaskiya kan gaskiyar halin da ake ciki a Amurka dangane Koronar, ya janyo sabani tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Donald Trump, inda ya rika caccakar babban jami’in lafiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.