Isa ga babban shafi

Labour ta yi barazanar tilastawa Boris Johnson ficewa daga fadar gwamnati

Jam'iyyar Labour a Birtaniya ta yi barazanar tilastawa Fira Minista Boris Johnson ficewa daga fadar gwamnati nan take, biyo bayan murabus din da ya yi sakamakon adawa mai zafi daga majalisar ministocinsa.

Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson.
Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson. REUTERS - HENRY NICHOLLS
Talla

Johnson ya ajiye mukaminsa na shugaban jam'iyyar Conservative mai mulki a ranar Alhamis, bayan da mukarrabansa kusan 60 suka ajiye ayyukansu a kasa da sa'o'i 48, domin nuna adawa da mulkinsa da ya cece-kuce ya mamaye, ciki har da batun gaza magance tsadar rayuwa, da kuma karya dokar korona a watannin baya.

Sai dai Boris Johnson mai shekaru 58, y ace zai cigaba da rikon kwaryar mukamin na Fira Minista har sai an sami magajinsa.

Tuni dai tsohon ministan kudi Rishi Sunak, wanda murabus dinsa a ranar Talata ya yi tasiri kan sauran takwarorinsa da suka mara masa baya, ya kaddamar da yunkurinsa na neman maye gurnin Boris Johnson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.