Isa ga babban shafi

Jirgi mai saukar ungulu na kashe gobara ya yi hadari a gabar tekun Girka

Wani jirgi mai saukar Angulu na masu aikin kashe wutar dajin da ta barke a wasu sassan kasashen Turai ya fadi a gabar tekun kasar Girka, dai-dai lokacin da yake kokarin aikin kashe wutar.

Wani jirgi mai saukar Angulu na masu aikin kashe wutar dajin da ta barke a wasu sassan kasashen Turai ya fadi a gabar tekun kasar Girka, dai-dai lokacin da yake kokarin aikin kashe wutar.
Wani jirgi mai saukar Angulu na masu aikin kashe wutar dajin da ta barke a wasu sassan kasashen Turai ya fadi a gabar tekun kasar Girka, dai-dai lokacin da yake kokarin aikin kashe wutar. REUTERS - COSTAS BALTAS
Talla

Bayanan da kafafen yada labaran cikin gidan girka suka fitar na nuni da cewa an yi nasarar ceto mutane 2 cikin guda hudun da jirgin ya fadi da su, kuma ana ci gaba da aikin neman sauran mutane biyu.

Wani kwararre kan harkokin yaki da annoba na kasar ya ce jirgin mai saukar Angulu ya doshi dajin Samos don tarar da takwarorin sa dake kokarin kashe wutar dajin da ta tashi a yankin.

Bayani na cewa wutar ta tashi a kasar ne da Misalin Karfe 11 na safiyar ranar Laraba agogon kasar, kuma tuni aka aike da jirage masu saukar Angulu guda uku da kuma masu aikin kashe gobara guda 50 don shawo kan ta.

To sai dai kuma wata kakkarfar guguwa dake kara rura wutar na zama barazana ga aikin masu kashe wutar, yayin da kasashen Turai ke ci gaba da fama da tsananin zafi da ya zarta Ma’aunin Celcius 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.