Isa ga babban shafi

Norway ta sake kame wani dan kasar Rasha da kurman jirgi a karo na biyu

Kasar Norway ta sanar da kama wani dan kasar Rasha dauke da jirgin sama mara matuki da na’urar daukar hoto bayan da aka gan shi yana daukar hotunan wani filin jirgin sama a arewa mai nisan kasar, wanda karo na biyu kenan da mahukunta ke makamaicin wannan kame cikin mako guda.

Wani jirgin sama mara matuki da 'yan sandan Faransa suka yi amfani da shi a Nice.
Wani jirgin sama mara matuki da 'yan sandan Faransa suka yi amfani da shi a Nice. Foto: REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Hukumomi basu bayyana sunanan dan kasar Rashan mai shekaru 51, da aka kama ranar Juma'a ba, bisa zargin amfani da jirgi mara matuki a kasar Norway, wanda tuni ya amsa laifinsa, inji su.

Sanarwar da rundunar ‘yan sanda a garin Tromso da ke arewacin kasar ta fitar ta ce, jami’anta sun kwace kayan aikin daukar hoto da dama da suka hada da jirgin sama mara matuki da kuma katin a dana bayanai.

Cikin abubuwan da aka kwace a tare da shi, har da  hotunan wani filin jirgin sama a garin Kirkenes da ke arewacin kasar da kuma na wani sansanin jirage masu saukar ungulu na sojojin Norway dake Bell, in ji sanarwar.

Kasar ta Scandinavia da wasu kasashen yammacin duniya da dama, sun haramtawa Rashawa wuce gona da iri kan abubuwan da suke cillawa sama tun bayan mamayar Ukraine a watan Fabrairu.

Kamen farko

A ranar Juma'ar da ta gabata 'yan sandan Norway sun ce sun kama wani dan kasar Rashan yayin tsallaka kan iyakar arewa mai nisa a farkon wannan mako lokacin ya dawo gida dauke da jirage marasa matuka biyu da tarin hotuna da bidiyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.