Isa ga babban shafi

Ana gudanar da zaben Shugaban kasa zagaye na biyu a Cyprus

A yau lahadi ne al'ummar Cyprus suke kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa,zaben da zai kasance kalubale ga duk jam’iyyar da za ta lashe shi a wani shiri na yaki da hauhawar farashin kayayyaki da cin hanci da rashawa.

Zaben kasar Cyprus
Zaben kasar Cyprus © Petros Karadjias/AP
Talla

An bude rumfunan zabe 1,113 da misalin karfe 7 na safe agogon kasar a yau lahadi.Zagaye na biyu da zai hada Nikos Christodoulides, mai shekaru 49, wanda ya jagoranci diflomasiyyar kasar tsakanin 2018 da 2022, ya zo na daya a zagayen farko da kashi 32.04% na kuri'un da aka kada, sai abokin takarar as dan gaban wani gogaggen jami'in diflomasiyya, Andreas Mavroyiannis, mai shekaru 66 (29.59%), tsohon jakadan Faransa da Ireland.

Nikos Christodoulides, da ke samun goyon bayan jam'iyyu masu tsatsauran ra'ayi, da Andreas Mavroyiannis, wanda ke samun goyon bayan jam'iyyar gurguzu Akel, sun tsaya a matsayin 'yan takara masu zaman kansu. Jam'iyyar Disy mai ra'ayin mazan jiya ta yanke shawarar kaucewa mara baya ga wani dan takara  bayan kayen da shugabanta Averof Neofytou ya sha a zagayen farko na ranar 5 ga watan Fabrairu.

A wurin jefa kuri'a na makarantar firamare ta Agios Antonios a Nicosia, Dora Petsa, 75, 'yar fansho da ta zo don kada kuri'a tare da danginta, tana tsammanin shugaban kasa na gaba "ya daidaita batun kasar.

Wanda ya lashe zaben zai gaji shugaban na hannun daman Nicos Anastasiades, mai shekaru 76, wanda ke kammala wa'adi biyu na shekaru biyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.