Isa ga babban shafi

Rasha ta kama dan jaridar Amurka kan zargin leken asiri

Hukumar tsaron cikin gidan Rasha ta ce ta kama wani dan jarida Ba’Amurke da ke aiki da mujallar Wall Street Journal a kasar kan zargin yi mata leken asiri a madadin Amurka.

Gwamnatin Rasha tana sa kafar wando guda da wadanda ke caccakarta.
Gwamnatin Rasha tana sa kafar wando guda da wadanda ke caccakarta. via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Sanarwar ta Alhamis wata alama ce ta kokarin da gwamnatin Rasha ke yi na dakile masu caccakarta, lamarin da ta zafafa aiwatarwa tun bayan da ta kaddamar da mamayar soji a Ukraine a shekarar da ta gabata.

Hukumar tsaron ta Rasha ta dakile wasu ayyukan da dan jaridan kasar Amurkan, Evan Gershkovich, ke yi ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa ma’aikacin na  mujallar Wall Street Journal  yana yi wa gwamnatin Amurka ne aiki.

Mujallar Wall Street Journal ta damu matuka a game da lafiyar Gershkovich, kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta  Reporters Without Borders (RSF) ta ce ta kadu a game da kama wannan dan jarida, wanda ta ce ya yi kamanceceniya da ramuwar gayya.

Kungiyar  RSF ta ce Gershkovich yana bincike ne a kan kamfanin tsaro mai zaman kanta, Wagner, wanda ke taka mahimmiyar rawa a yakin da Rasha ke yi a Ukraine.

Hukumar tsaron cikin gida Rashar ta  tabbatar da cewa  Gershkovich, mai shekaru 31 wanda ke aiki da  tantancewar ma’aikatar harkokin wajen Rasha ya shiga hannunta ne saboda zargin yana tattara bayanai a kan ayyukan sojin Rasha.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova ta ce an kama Gershkovich dumu-dumu cikin aikata  abin da ake zarginsa da shi.

Kafin komawa Wall Street Journal, Gershkovich ya yi aiki da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Yan jin harsunan Ingilishi da Rashanci sosai, kuma ya taba aiki da a matsayin wakilin shafin labarai na Moscow Times, wanda ke wallafa labarai da  harshen Ingilishi.

Iyayensa sun koma Amurka tun yana yaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.